Ya kautu iyaye su taimaka su sanya ‘yaya mata a makaranta domin al'umma ta amfana da ilimin diya mace, inji wata matashiya malama Fatima Idris, a zantawarsu da wakiliyar DandalinVoa, Baraka Bashir.
Ta ce lokaci yayi da iyaye zasu daina dorawa 'yayansu tallace tallace domin neman abin duniya, tana mai cewa ilimi ne kadai abinda zai fitar da diya mace daga kunyar duniya tare da kara mata kima a idon al'umma.
Malama Fatima ta kara da cewar babban burinta a matsayinta na mace shine ta sami ilimi hakan ce ma ta sa ta jajirce har ta kai ga kammala digirinta domin al'ummarta ta amfana da iliminta mussamam ma a fannin da ta zabawa kanta na aikin jarida.
Fatima ta ce radiyo ta fi kowacce kafar sadarwa isar da sako ta kara da cewar sai ta ta fara yin Diploma kafin ta samu damar yin digirinta, amma hakan bai sanyaya mata gwiwa ba.
Your browser doesn’t support HTML5