Wannan na zuwa ne lokacin da dalibai da malaman makarantun furamare da islamiyoyi ke ci gaba da more tallafin da hukumar UNICEF ke bayarwa ga makarantu, Kafin karewar wa'adin bayar da tallafin.
Hukumomi dake kula da sha'anin ilimi sun yi ta fitar da alkalumman da ke nuna miliyoyin yaran da suka isa zuwa makaranta amma basu zuwa makaranta musamman a arewacin Najeriya.
Hakan na faruwa ne duk da kudaden da gwamnatoci ke ware wa bangaren ilimi, abinda ya zaburar da hukumomin bayar ta tallafi na kasashen duniya kawo dauki domin ceto yaran.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ‘ masu ruwa da tsaki kan harkar iliimi na ci gaba da fargabar yanayin da ilimi matakin farko, kan iya shiga muddin bai ci gaba da samun kulawa ba yadda ya kamata.
Asusun UNICEF ya aiwatar kuma yana kan aiwatar da ayyukan da za su taimaka da nufi bunkasa harkokin ilimi ta hanyar bayar da tallafi a fannin inganta karatun yara, daya daga cikin shiraye-shiryen shine wanda ke gudana yanzu na bunkasa karatun ‘yan mata a jihohin Sakkwato da Zamfara.
Duk da haka akwai bukatu da malaman ke ganin samun biyansu kan iya kara inganta ilimin yara.
Abin fargaba dai bai wuce yadda makarantun zasu iya komawa ba, idan ‘unicef’ ta kammala wa'adin aikin ta, duba da yadda gwamnatoci ke nuna karamcin kulawa da ilimi a Najeriya.
Masu ruwa da tsaki a harkar ilimi na ganin akwai bukatar gwamnatoci su kara daukar matakai na ganin dorewar nasarorin da aka samu a fagen samar da ilimi ta yadda za'a ci gaba da samar da dalibai wadanda zasu iya kawo ci gaban yankunan su da kasa baki daya.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5