Ilimantar Da 'Ya Mace Tamkar Ilimantar Da Alumma Ne- Inji Khadija

Khadija Shua'ibu

Khadija Shu’aibu matashiya wacce ta karanci karatun likitanci a wata jami’a a kasar Misra ta kuma nemi kwarewa a fannin matsalolin mata.

Ta ce tun da farko ta fara neman gurbin karatu ne a jamiar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ta rubuta jarrabawar JAMB sau biyu bata samu nasara ba daga bisani ta samu gurbi karatu a kasar Misra.

Khadija ta ce ta kasance tun tana 'yan karamar yarinya take da sha’awar zama likita ta kuma bayyana cewa akwai bambanci karatu a Misra da gida Nijeriya, domin kuwa a cewar ta a can babu wata matsala ta wutar lantarki komai a tsare yake, akwai lokacin karatu da cin abinci komai an ware masa lokacinsa.

Fanninta dai shine fannin mata masu ciki da matsaloli na mata kuma a yanzu haka ta zana wata jarabawa wadda zata tabbatar da cewar ta karanci likitanci kafin ta fara gudanar da aiki a Najeriya..

Khadija taja hankalin mata da su jajirce wajen neman ilimi sannan ta ja hankali iyaye da su baiwa yayansu limi a cewarta ilmantar da diya mace tankar an ilmantar da al’umma ce baki daya.

Your browser doesn’t support HTML5

Ilimantar Da 'Ya Mace Tamkar Ilimantar Da Alumma Ne- Inji Khadija