Wata matashiya Amina Yakubu Abdullahi, ta ce sana’ar sayarda takalma ya taimakamata alokaci da take karatun ta na Jami’a ta ta ce a yayin da take zango na biyu a jami’a ne wani abokinta dalibi da yake fita kassahen waje, yake bata kaya ta sayar daga bisani ta biya a haka ne ta tara jarinta na kanta.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da Baraka Bashir, wakiliyar DandalinVOA a birnin Kano.
Ta ce tana da muradin tara kudaden alawus da ake basu na yi wa kasa hidima domin sake dawo da sana’ar da take yi a da , wanda ya karye sakamakon bashin daga masu saye.
Ta kara da cewa da wannan sana’ar ne ta ke kashe wa kanta kananan bukatu maimako mikawa iyayen dawainiyar ta na yau da kullum.
Amina ta ce tana fatan idan ta tara kudadenta zata fara sabon sana’a domin kasancewa mai dogaro da kai a koda wane lokaci.
Your browser doesn’t support HTML5