A wata hira ta musamman da yayi da Gidan telebijin din Channels mai zaman kansa a Najeriya, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce idan Majalisar dokokin kasar tana so ya sa hannu a dokar zabe na shekara 2021, sai ta sake yi wa dokar gyara.
Wani abu da Shugaban Kwamitin Kula da Hukumar zabe a majalisar dattawa ya ce majalisar za ta yi zama na musamman akan dokar bayan ta dawo hutu.
Sai dai ga wani mai nazari a al'ámuran yau da kullum yana ganin majalisar kasar ta kawo rudani ne da gangan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce abu daya tilo da ya fi daukan hankalinsa shi ne batun 'yar tinke ko kato bayan kato, inda ya ke ganin ba daidai ba ne a ba mutane umurni a mulkin dimokradiya.
Buhari ya ce ya kamata a samu zabi ba wai a fitar da gwani kai tsaye ta hanyar tilasta wa mutane ba.
A lokacin da yake wa Muryar Amurka bayani a game da matsayin majalisar dattawa akan wanan batu, shugaban kwamitin kula da hukumar zabe na majalisar dattawa, Kabiru Ibrahim Gaya ya ce dukannin fanonin da abin ya shafa a Majalisar kasa za su yi zama na musamman domin sake duba dokar
Amma ga mai nazari a al'amuran yau da kullum Abubakar Aliyu Umar, ya yi suka ne akan matakin da majalisar ta dauka tun farkon gyara da suka yi wa dokar zaben, inda ya nuna cewa majalisar dokokin kasar ta kawo rudani ne da gangan, a bisa wasu dalilai na su.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayana rashin tsaro da tsadar kudin gudanar da zaben fid da gwani a tsarin 'yar tinke ko kuma kato bayan kato, a matsayin dalilan sa na kin amincewa da kudurin dokar, bayan ta kwashi tsawon wata daya a hanun sa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5