ICPC Ta Hada Kai Da Jihohin Najeriya Don Yaki Da Cin Hanci

Shugaban ICPC Barr. Musa Adamu

Hukumar ta ICPC da kan yaki cin hanci a tsakanin jami'an gwamnati ta sha alwashin sakamakon taron ba zai zama zane kan ruwa ba.

Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta hada kai da jihohin Najeriya don karfafa tasirin yaki da cin hanci daga tushe.

A taron wuni daya a Abuja, ICPC ta ce hakika kwamishinonin shari'a na jihohi na da gagarumar rawar takawa a yaki da almundahana.

Taron wanda ya samu halarar Ministan Shari'a Lateef Fagbemi da tsohon Minista Kanu Agabi ya ja hankalin kwamishinonin da cewa lallai gwamnoni na sauraron shawararsu don haka ya dace su yi amfani da damar wajen kawo gyara.

Shugaban hukumar ta ICPC Barista Musa Adamu ya ce nadama kan biyo bayan ga duk jami'in da ke da alhakin gyara amma ya yi kasa a gwiwa "lokacin da muka bar kujera ko tsufa ya same mu za mu ga abubuwan da ya dace mu yi to in kuwa ba mu yi ba tarihi ba zai yafe mana ba"

Mahalarta taron da hukumar ta ICPC ta shirya

Kwamishinan shari'a na jihar Yobe Barista Saleh Samanja ya ce yaki da cin hanci kan samu nasara ne ba a lokaci daya ba don haka za a cimma nasara ta hanyar jajircewa.

Hakanan shi ma Kwamishinan shari'a na jihar Jigawa Barista Bello Fanini ya ce aikin na kwamishinonin yana da muhimmaci wajen saita yaki da rashawa a matakin na jiha kasancewar su masana lamuran shari'a.

Hukumar ta ICPC da kan yaki cin hanci a tsakanin jami'an gwamnati ta yi alwashin sakamakon taron ba zai zama zane kan ruwa ba.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

ICPC Ta Hada Kai Da Jihohin Najeriya Don Yaki Da Cin Hanci.mp3