ICPC Ta Gano Almundahanar Naira Biliyan 300 A Wasu Sassan Najeriya

ICPC

Yaki da cin hanci da almundahana da dukiyar al'umma da gwamnatin Najeriya ke ikirarin tana yi a tsawon shekaru bakwai, bai hana wadannan munanan ayukka gudana ba a sassa daban na kasar.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta ce ta gano almundahna ga ayukkan mazabu na ‘yan majalisar tarayya ta sama da Naira biliyan 300 a sassan kasar, inda a Sokoto kadai ta gano ayyuka da aka boye ba ‘a yi wa jama'a ba, na fiye da naira biliyan uku.

Lokacin dimokradiya ne ya kamata ‘yan kasa su amfana da ayyukan raya kasa da ci gaban al'umma, domin ko bayan ayyukan da gwanonin jihohi ke tsara aiwatarwa a kasafin kudin da suke yi kowace shekara, ‘yan majalisar dokokin tarayya ma suna da ayyukan mazabu da suke sakawa a jadawalin ayyukan da zasu aiwatar a mazabunsu kuma gwamnati ta bada kudin aiwatar da ayyukan.

Duk da yake a Najeriya wasu sukan aiwatar da ayyukan yadda suka tsara, wasu kuwa akan samu tangarda ta almandahana wajen aiwatar da ayukkan.

A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya kadai hukumar da ke yaki da cin hanci ta ICPC tace ta bankado wasu ayyukan mazabu na ‘yan majalisar tarayya da aka yi almandahana na fiye da naira biliyan ukku, acewar Shugaban hukumar a Sakkwato Garba Tukur Idris.

Wani abu da hukumar ta ICPC ke ganin kan iya taimakawa wajen rage yin almandahna da ayyukan da ya kamata a yiwa jama'a, shi ne wadanda ake yiwa ayyukan su ringa sa ido yadda ya kamata domin, ayyukan da ake gudanarwa da dukiyar gwamnati ayyukan su ne.

Shugaban hukumar ICPC ya ce suna son jama'a su shiga cikin ayyukan da ake yi musu, saboda ICPC kadai bata iya hana cin hanci da rashawa da almandahana ba a Najeriya, duk aikin da ake yi al'umma su sa ido, abinda suka ga basu gane ba su tuntubi hukumar ta ICPC ita ta san abinda zata yi.

Kuma ya kamata duk abinda za’a yi cikin karamar hukuma ya zamo an sanar da ita hukumance domin ta a san abinda za'a yi da yadda za'a yi shi da dalilin yin sa.

To ko wayar da kan jama'a akan sanin cewa ayyukan da ake aiwatar musu da dukiyar gwamnati na sune, kan iya kawo sauyi ga almandahna da ake yi wajen aiwatar da ayyukan, kamar yadda ICPC ke fadakarwa akai?

Mai sharhi akan lamurran yau da kullum Farfesa Bello Badah, ya ce basu iya yin haka, domin tun farko ba'a saka su cikin ayyukan ba, ba'a nuna suna da muhimmanci ba, ba'a nuna musu dukiyar kasa tasu ce ba, ayi musu abinda ke zama ci gaba gare su ba, domin yanzu jama'a basu iya ko tambayar wakilan su akan su san wakilcin da suke yi musu ba.

Cin hanci da rashawa dai da jimawa masana ke fadar shine babban abin da ya durkusar da Najeriya.

Saurari rahoto daga Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

ICPC Ta Gano Almandahana A Ayyukan Wasu Sassan Najeriya Na Sama Da Naira Biliyan 300.mp3