Malam Bahaushe na da wata al’ada ta rarraba azumi kashi uku, wato goma na marmari, goma na wuya da goma na dokin sallah. Galibin jama’a da sun shiga goma ta wuya sai ibadar ta fara yi masu nauyi.
A tattaunawar da DandalinVOA yayi da wasu mutane dangane da goma ta wuya, wasu sun tabbatar da yadda suke jin nauyin ibada a goma ta wuya, wasu kuma sun ce basa jin nauyin ibadar sa dai ma su kara kwazo don samun lada.
Muhammadu Sani Ahmad, na'ibin masallacin Shiek Jafar da ke unguwar Sabuwar Gandu a birnin Kano dake Najeriya, ya bayyana cewa babu wani kashe kashe na ibada a lokacin azumin ramadana a musulunci. Ya kuma ce azumi wajibi ne ga musulmi, amma wadanda azumin ke basu walaha, an basu dama su ciyar da miskinai amma kuma bai dace ba mutum ya fake da wata ‘yar larura don kaucewa azumi.
Saurari cikakken bayani cikin sauti daga Baraka Bashir
Your browser doesn’t support HTML5