Hussaina Sulaiman mai sana’ar guga a cikin gida ta shafe shekaru kimanin sha bakwai tanayi, a matsayin sana’ar hannu domin samun zaman kai.
Tace ta fara ne sakamakon yadda take shan wahala wajen neman gugan mai gidanta, ga matsalar rashin wuta da ake fama da ita a yankin su, sobada hakane ta ga mai zai hana ta kama sana’ar a matsayin abin yi.
Tace kamar wasa a haka ta fara har Allah ya albarkaci sana’ar, ta fara samun guga daga makwabtanta. Sannu a hankali, haka har aka santa ta fara wannan sana’a wanda a kowanne riga tana karbar naira goma kudin guga.
Ko da ta fara, sai abin ya rika ba mutane mamaki, yaya za’a yi a ce mace tana sana’ar guga. Sana’ar da aka fi alakata da maza. To amma tun ana tunani ba zata iya ba, har aka yadda da kwazonta, da kokarin cika burinta.
Ko a yanzu tana da akalla mutane kimanin biyar da suke wannan sana'ar da ita a gidan da take.
A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5