Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Na Yankin Afrika Ta Yamma Na Taro A Nijar

Taron kungiyar ta NACIWA (Network of National Anti corruption Institutions in west Afrika)  ko RINLCAO.

Shuwagabanin hukumomin yaki da cin hanci daga kasashen Afrika ta yamma suna gudanar da taron wuni 1 a birnin Yamai a karkashin inuwar kungiyarsu ta NACIWA ko RINLCAO.

Ana gudanar da taron ne da nufin tantauna hanyoyin karfafa matakan yaki da wannan mummunar dabi’a da ke dabaibaye ci gaban tattalin arziki.

Lura da yadda mahandama da masu cin hanci ke yada ayyukansu daga wannan kasa zuwa waccan ya sa hukumomin yaki da cin hanci a yankin Afrika ta yamma hada guiwa domin tunkarar wannan al’amari saboda haka wannan taro zai karkatar da akala wajen karfafa matakan da zasu taimaka a cimma nasara a wannan yaki.

Taron kungiyar ta NACIWA (Network of National Anti corruption Institutions in west Afrika) ko RINLCAO.

Shugaban hukumar EFFC ta Najeriya Abdulrashid Bawa shine shugaban rikon kungiyar NACIWA ko RINLCAO. Ya ce sha'anin aikin yaki da cin hanci da rashawa ya wuce na kasa daya saboda a ko da yaushe mutane kan fitar da kudade zuwa kasashen ketare.

Taron kungiyar ta NACIWA (Network of National Anti corruption Institutions in west Afrika) ko RINLCAO.

Anobar Covid din da aka yi fama da ita a shekarun nan 2 ta haddasa tsaikon wajen tafiyar da ayyukan NACIMA a tsawon wannan lokaci dalili ke nan kasashe mambobin kungiyar suka hallara a Abuja a watan Maris din da ya gabata don farfado da ayyuka.

Mahalartan zaman na birnin Yamai za su jaddada shawarwarin da aka tsayar a waccan haduwa wanda ko shakka babu za su yi tasiri sosai wajen dakile hanyoyin wawurar kudaden a wadanan kasashe.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

TARON HUKUMOMIN YAKI DA CIN HANCI NA AFRIKA TA YAMMA.mp3