Hukumomin Tsaro Da Gwamnatin Jihar Taraba Sun Mai Da Martani Ga Sanata Bwacha

Ga me da kalaman wani dan majalisar dattawa dake wakiltar mazabar Taraba ta Kudu, Sanata Emmanuel Bwacha, yayi a makon jiya a zauren Majalisa cewa yanzu haka ‘yan Boko Haram na shigar fulani makiyaya ana shigo da su a manyan motoci zuwa Arewacin jihar.

Wannan kalamai ya tada hankalin al'umman yankin lamarin da ya kai rundunan yan sandan jihar kiran wani taron manema labarai game da batun, yayin da kungiyoyi suma ke cigaba da maida martani kan wannan magana.

Hukumomin tsaro da kuma gwamnatin jihar sun musunta wannan batu, a wata ganawarsu da manema labarai. Kwamishinan ‘yan sandan jihar PC Sha’aibu Alkali, ya kuma nemi al’ummar jihar Taraba da su kwantar da hankulansu.

Shima gwamnan jihar Taraba, yace gwamnatin jihar a tsaye take wajen kare rayuka da dukiyar mutanen jihar.

An dai sha samun rikicin Fulani da Makiyaya da kuma ‘yan kabilar Jikku manoma a kudancin jihar, yankin da shi ‘dan majalisar ya fito, kuma wannan ne ma yasa hadakar kungiyar makiyaya ta Myatti Allah, mai da martani game da wannan zargi. Saurari cikakken rahotan.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Tsaro Da Gwamnatin Jihar Taraba Sun Mai Da Martani Ga Sanata Bwacha - 7'04"