Hukumomin Nijar Sun Kama Gwamman Mutane Da Laifin Yada Kalaman Kabilanci

Sojojin Nijar

Gwamnatin mulkin sojan Nijer ta gargadi ‘yan kasar su kasance masu nuna halin dattako ko kuma su fuskanci fushin hukuma bayan da tace ta lura da yadda wasu ke yada manufofin kabilanci da na jihanci a kafafen sada zumunta.

Tuni aka kama wasu gwamman mutane da laifin yada irin wannan haramtacciyar dabi’a wace mahukunta suka ce ta samo asali daga wasu kalaman da shugaban Macron na Faransa ya yi a washegarin kifar da Mohamed Bazoum.

A taron manema labaran na hadin guiwa da suka kira, Ministan shara’a Alio Daouda da takwaransa na cikin gida Janar Mohamed Toumba da magatakardan ofishin Ministan sadarwa Moustapha Tinao sun sanar cewa, abubuwan da ke faruwa a kafafen sada zumunta a halin yanzu sun fara wuce gona da iri ganin yadda a fili karara masu amfani da irin wadanan hanyoyi na sadarwa ke furta kalaman nuna kyama ga wannan ko waccan kabila duk kuwa da cewa dokokin Nijer sun haramta irin wannan dabi’a. Hukumomin sun ce sun cafke wasu wadanda ake zargi da aikata irin wannan laifi.

Wannan al’amari na nuna kiyayya a tsakanin kabilu da wasu masu amfani da kafafen sada zumunta ke fakewa da shi, abu ne da hukumomin mulkin Sojan Nijer ke zargin Faransa da assasawa inji ministan cikin gida Janar Mohamed Toumba.

Yace "kun ji yadda a wani lokaci shugaba Macron ya yi yunkurin kabilantar da juyin mulkin da CNSP ta yi. Abu ne wanda ya saba wa hankali domin ba za ta yiwu a ce ‘yan Nijer su na goyon bayan hambararren shugaban kasa kuma a zarge su da kabilanci ba, ba za kuma zargin ‘yan Nijer da kabilanci ba alhali sun zabi shugaban da kabilarsa ta sha bamban da kashi 98 daga cikin 100 na yawan al’ummar wannan kasa. Wannan kawai yunkuri ne na amfani da dadaden salon da suka saba fakewa da shi don cimma manufofinsu wato a raba kan jama’a don jin dadin gudanar da mulki."

Ofishin Ministan na shara’a da na Ministan cikin gida da na Ministan sadarwa sun karkare wannan taron manema labarai da tunatar da ‘yan kasa game da hukunce hukunce da doka ta yi tanadi da suka hada da biyan tara da zaman gidan wakafi ga duk wanda aka kama da laifin furta kalaman kabilanci ko jihanci da wadanda ke amfani da kafafen zamani don cin zarafin wani ko yada bayanan da ke barazana wa zaman lafiyar al’umma.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Nijar Sun Kama Gomman Mutane Da Laifin Yada Kalaman Kabilanci