Dukkan Ministoci da manyan darektocin da ke da hannu a maganar yaki da bara a matsayin sana’a ne suka hallara a babban taron da Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou ya jagoranta da zummar tattauna hanyoyin da za a bullowa wannan al’amari da ke kokarin fin karfin matakan da aka dauka a baya.
Firai Ministan na Nijer yace wannan yaki za a yi shi a cikin gida da waje, matakan da za a dauka domin tunkarar wannan matsala misali ne na yadda abin yake a kasashen waje wadanda tun da dadewa suka haramtar da bara. A irin wadannan kasashe an kafa cibiyoyin ajiyar mabarata inda idan aka yi katarin kama mutun sau biyu saboda laifin bara ba zai sami kulawa daga ofishin jakadancin kasarsa ba, saboda haka ba makawa hukunci zai hau kansa daidai da dokokin da wannan kasa ta tanada.
“A Nijer shirin da muka sa gaba shi ne ya kamata mu fara tunanin kafa cibiyoyin ajiyar mabarata da nakasassu ta yadda za a ajiye mabaratan da aka hana ketara iyaka kafin kammala aikin tantancewa don mayar da su garuruwansu na asali,” a cewar Firai Ministan.
Ya ci gaba da cewa mun tanadi dukkan matakan da zasu ba mu damar samun nasarori a wannan yaki, muna da takardu da dama. Akwai dokokin hukunta mabarata da dillalan da ke fitar da su zuwa kasashen waje saboda haka ya kamata a yi tsayin daka don tabbatar da doka. Haka kuma mun umurci jami’an tsaro su tsaurara matakai akan iyakokinmu mun kuma basu dama idan suka ga gungun mabarata na kokarin ketara iyaka to kada su bari su tsallaka su kuma dauki matakan mayar da su yankin da suka fito.
Dubban mabarata ne gwamnatin Nijer ta kwaso daga Senegal da Ghana a bana, galibinsu mata da yara kanana. Girman wannan matsala ya sa kungiyoyi masu zaman kansu irinsu ONG GRASPI suka shiga yunkurin fadakar da jama’a kan kaskancin da ke tattare da bara.
A sabon shirin da ta sa gaba, gwamnatin Nijer a cewar Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou, za ta fara ne da aiyukan waye kai sannan a mataki na biyu za a fara hukunta wadanda aka samu da laifin bijirewa doka, sai mataki na uku wanda zai ta’allaka kan yi wa mabaratan rakiya da nufin fitar da su daga harkar bara, dabi’ar da aka yi amannar cewa haramtacen abu ne da wasu ke neman mayar da shi madogara.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5