NIAMEY, NIGER - Tawagar jami’an gwamnatin ta kuma yada zango domin jajanta wa jama’a sakamakon rasuwar wasu manoma kimanin 12 da ‘yan bindiga suka hallaka a ranar Alhamis din da ta gabata.
Dubban mazauna kauyuka da dama na karamar hukumar Ouro Gueladio ne ke samun mafaka a garin Torodi yau makwanni a kalla biyu bayan da ‘yan ta’adda suka ba su wa’adin ficewa kokuma su dauki tsauraran matakai akansu; mafari kenan Ministan cikin gida Hammadou Souley Adamou ya kai ziyara a sansanin wadanan mutane domin basu kwarin guiwa.
“Mun zo dauke da sakon karfafa muku guiwa da goyon bayan shugaban kasa kuma mu kara jaddada maku aniyar warware wannan matsala cikin hamzari don ganin zaman lafiya ya dawo a wadanan gundumomi biyu na kasarmu wato Say da Torodi.” In ji Adamou.
Ministan ya kara da cewa gwamnatin Nijar ta kudiri aniyar gudanar da wasu manyan ayyukan da za su ba da damar samar da ci gaba a wannan yanki.
Ya kara da cewa, a karkashin shirin bunkasa hada-hadar kasuwanci a tsakanin tashar jirgin ruwan Lome zuwa Ouaga da Niamey za su gudanar da ayyuka da dama na ci gaban al’umma da suka shafi wadanan gundumomi inda za su kashe million 20000 na cfa don gina hanyoyin zurga-zurga na karkara bayan ayyukan gina makarantu 132 da asibitoci, wanda ya ce saboda haka suke kiran ‘yan asalin wannan yanki musamman shugabanin al’umma su sa himma.
Jihar Tilabery da ke makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso na fama da aika-aikar kungiyoyin ta’addanci inda ko a ranar Alhamis din da ta gabata ‘yan bindiga suka kashe manoma 12 a gonakinsu abinda ya sa tawagar Ministan cikin gida zuwa inda ya faru wato karkarar Anzourou domin jajantawa jama’a tare da basu kwarin guiwa.
Lamarin tsaro a wannan yanki da kasar Faransa ta girke wani bangare na sojojinta da ta kwashe daga Mali da sunan dafa wa dakarun Nijar a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’adda na daure kan daukacin ‘yan kasar da ke mamakin yadda matsalar ke kara ta’azzara.
A taronsu na farkon watan nan na Yuli, Shugabanin kasashen Kungiyar CEDEAO sun nanata aniyar kafa rundunar hadin guiwa don yaki da ta’addanci sakamakon lura da abinda suka kira kalubalen da ke barazanar mamaye baki dayan yankin a yayinda talakkawa a nasu bangare ke ganin kamar ana jan kafa.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5