Hukumomin Nijar Sun Kaddamar Da Ayyukan Gina Rijiyoyin Burtsatse A Karkara

Wasu masu debo ruwa daga rijiya

Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta kaddamar da ayyukan gina daruruwan rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana a yankunan karkara musamman wadanda ke fama da matsalar ruwan sha da nufin samar wa al’umma wadataccen ruwa mai tsafta.

NIAMEY, NIJAR-Wannan wani bangare ne na ayyukan da gwamnatin tace ta sa gaba don kyautata rayuwar ‘yan kasar.

A karkashin wani shirin hadin gwiwa da abokan ayyukan gina wadanan daruruwan farage ko kuma rijiyoyin burtsatse a yankunan da ake dauka a matsayin mafiya fama da karancin ruwan sha a kasar.

Karancin ruwa a Nijer

A hirar shi da Muryar Amurka, Malan Mamman Ibrahim Mahaman Ministan ayyukan raya karkara ya bayyana cewa, shugaban kasa ne ya basu umarnin su kaddamar da wannan tsarin inda suka hada gwiwa da sashen da ke kula da ruwa na kasar Nijar, kuma za su gina su a dukan wurare da ke matsalolin ruwa sosai kamar jihar Tahoua, jihar Zinder, Maradi, Dosso da kuma Tilabery.

Karancin ruwa a yankunan karkara na daga cikin matsalolin da ke haddasa tashe tashen hankula a tsakanin jama’a saboda haka ake ganin wannan shiri zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya.

Million 1800 na cfa ne za a kashe domin ayyukan gina wadanan rijiyoyin burtsatse da aka fara da jihar Tilabery.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Nijer Sun Kaddamar Da Ayyukan Gina Rijiyoyin Burtsatse A Karkara