Najeriya tana daga cikin kasashen da a 'yan shekarun nan ke fama da matsalar ruwa, na noman rani ko wanda al'umma za su yi aiki da shi kamar sha ko ayyukan yau da kullum.
abuja, nigeria —
Ministan albarkatun ruwa na Najeriya Suleiman Adamu ya ce ma'aikatar ruwa ta tarayya na bukatan Naira biliyan 26 wajen ganin an magance karancin ruwa a kasar, amma manazarta na ganin samar da wadatacen ruwa ba aikin gwamnatin Taraiyya ba ne.
Wannan matsala ta ruwa ta haifar da bullo da amfani da ruwan gora ko roba ko ruwan leda wanda aka fi sani da pure water a turanci.
Hakan ya sanya manazarta tunanin ko menene aikin ma'aikatar ruwa ta tarayya da jihohi kenan?
A hirar shi da Muryar Amurka, manazarci a siyasar tattalin arziki da cigaban kasa Nasiru Marmara yana ganin wannan fanin ya dan samu matsala a Najeriya saboda wasu dalilai da suka hada da cewa ba ko ina ba ne ake samun wadataccen ruwa, domin mahukunta basu kula da madatsun ruwa ba, ko kuma an bar su sun lalace.
Nasiru ya ce ba a fadada hanyoyin samun ruwan famfo ba, saboda a yanzu an samu karuwa na mutane a ko ina.
A nashi bayanin, Ibrahim Jalo yana ganin bai kamata Gwamnatin Tarayya ta zama mai daukan nauyin samar da ruwa a kasa ita kadai ba domin yana ganin kananan hukumomi ne ke da alhakin samar da wadattacen ruwa ga al'umma, amma matsalar ya kara tsananta ne domin gwamnoni sun yi wa ayyukan kananan hukumomi katsalandan. Bisa ga cewarsa, sun mayar da kananan hukumomi wani bangare na gidajen su, saboda haka ba sa aiki yadda ya kamata.
Akan haka ne Muryar Amurka ta tuntubi Ministan Kula da Ma'aikatar Ruwa ta taraiyya Injiniya Suleiman Adamu a wajen kare kasafin kudin ma'aikatar na badi a gaban kwamitin albarkatun ruwa na Majalisar Dattawa, wanda ya kai Naira Biliyan 26.
Suleiman Adamu ya ce ma'aikatar sa ta bullo da wasu dabaru da za su taimaka wa kasa wajen samun wadattacen ruwa na noma, walau na ayyukan tafiyar da ruyuwa na yau da kullum, har da ma na noman rani.
Ya ce ba aikin gwamnatin tarayyya ba ne samar da ruwa a jihohi amma tana iya ba jihohin tallafi domin su samu wadattacen ruwa.
Ministan albarkatun ruwa Suleiman Adamu ya kara da cewa akwai wata doka ta ruwa dake gaban Majalisar Dokoki, wanda idan an kammala aiki akan dokar zai inganta hanyoyi na gudanar da ayyukan albarkatun ruwa a kasar.
Saurari rahoton cikin sauti: