Hukumomin Nijar Sun Jaddada Aniyar Gudanar Da Bincike Kan Kisan Wani Dalibi

Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai

A Jamhuriyar Nijar alkali mai shigar da kara a kotun birnin Yamai ya jaddada aniyar samar da haske a game da kisan wani dalibin sakandare da ya rasu bayan da wani jami’in tsaro ya bude wuta akan wata motar  dalibai a ranar Talata.

Sai dai kungiyar dalibai ta kasa na cewa dole ne a wannan karon a yi hukunci a wannan mumunan al’amari da ke kokarin samun gindin zama a kasar.

Bayanai na cin karo da juna dangane da yanayin da wannan matashi Nouridine Alio ya rasu inda wasu ke cewa a lokacin da jami’an tsaro suka fatattaki motar daliban ne, daya daga cikinsu ya bude wuta yayin da wasu majiyoyi ke cewa wani jami’in dake gadi a gidan wani minista ne ya aikata kisan.

Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai

Lamarin da ya sa alkali mai shigar da kara Procueur de la Republique Chaibou Moussa kiran taron manema labarai. ‘Tun da abun ya faru suka tura 'yan sanda inda suka gudanar da bincike kan lamarin.’

Jami’an Tsaro Sun Kashe Wani Dalibi A Yamai

Kungiyar dalibai ta kasa USN wacce ta gudanar da taron gaggagawa a sanadiyar faruwar wannan al’amari ta bayyana takaicinta akan yadda kisan dalibai ya zama ruwan dare a nan Nijer.

Hassan Effred shi ne kakakin kungiyar dalibai USN, ya kuma ce ba zu yarda a turbude shi ba a yi bincike mai zurfi ba, dole ne a yi hunkunci dai-dai wa daidai ga dukkan wadanda hanunsu ke ciki, kuma kada a sa siyasa a so rai.

Babban mai shigar da kara yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da bincike.

Wannan al’amari na kisan dalibi Nouridine Alio na wakana ne a wani lokacin da kungiyar dalibai ke addu’oin tunawa da wasu ‘yayanta 3 da jami’an tsaro suka bindige a yayin zanga zangar dalibai ta ranar 9 ga watan fabrerun 1990 inda a yau larabar 16 ga watan fabreru daruruwan dalibai suka ziyarci makwantan wadanan mamata dake makarbar Yantala ta birnin Yamai.

Suna masu jaddada ci gaba da gwagwarmayar ganin an hukunta dukkan masu hannu a kisan abokansu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Nijer Sun Jaddadar Aniyar Gudanar Da Bincike Akan Kisan Wani Dalibi