A yayin ganawarsa da wakilan kafafen kasa da kasa ne ministan kiwon lafiyar al’umma, Dr. Iliyasu Idi Mainasara ya yi bayani game da halin da ake ciki a kauyukan yankin Maradi masu makwaftaka da garin Jibia dake Najeriya, inda a farkon watan jiya aka samu barkewar annobar cutar amai da gudawa da ake kira Cholera da turanci wadda ta janyo asarar rayuka da dama.
Binciken likitoci ya yi nuni da cewa amfani da ruwan gulbi a matsayin ruwan sha a wasu kauyukan Madarunfa ne ya janyo bullar cutar dake bazuwa tamkar wutar daji, a yayin da jama’ar Jibia suka tsinci kansu cikin matsalar ambaliyar ruwa cikin kwanakin baya, saboda haka mahukunta ke jan hankalin al’umma.
Tuni dai hukumomin kiwon lafiyar al’ummar Nijer da na Najeriya suka yanke shawarar hada guiwa da nufin fadakar da jama’a akan riga kafin cutar cholera a garuruwan gundumar Madarunfa da na karamar hukumar mulki ta Jibia.
Ministan kiwon lafiyar Janhuriyar Nijer Dr. Iliyasu Idi Mainasara ya tabbatarda cewa kawo yanzu, babu in da aka samu labarin bullar cutar cholera a sauran yankunan kasar in ban da wasu mutane 3 da aka gano a garin Maradi da ake jinya a asibiti.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma
Your browser doesn’t support HTML5