Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Dole Ne Zimbabwe Ta Yi Wasu Sauye-sauye


Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da Jakadan Amurka a Zimbabwen, Brian Nichols
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da Jakadan Amurka a Zimbabwen, Brian Nichols

Amurka ba za ta cire takunkumi da ta sakawa wasu manyan jami'an kasar Zimbabwe ba da suka hada da shugaban kasar na yanzu, har sai ta yi wasu sauye sauye a cewar Jakadan Amurka a kasar, Brian Nicholas

Jakadan Amurka a kasar Zimbabwe Brian Nicholas yace wajibi ne Zimbabwe ta dukufa wajen gudanar da sauye-sauye masu ma’ana muddin tana son Amurka ta cire wa manyan jami’an ta takunkumi.

Jakadan dai yayi wannan furucin sailin da ya ziyarci shugaban kasar Emerson Mnangagwa a fadar gwamnatin kasar dake birnin Harare.

Ziyarar ta tsawon sa’a guda tazo ne, sati guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump yasa hannu a wata dokar gyara demokaradiyya da inganta tattalin arzikin kasar Zimbabwe wanda ake kira ZIDERA.

Dokar dai ta sake sabunta takunkumin ne da Amurka tasa wa wasu mutanen kasar ta Zimbabwe dama wasu kanfanin ta, tun daga shekarar 2002.

Shima shugaban na yanzu Emerson Mnangagwa na cikin wanda wannan takunkumin ya shafa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG