Hukumomin Lafiya A Nijar Sun Bayyana Shirin Janye Tallafin Tiyatar Haihuwa

A jamhuriyar Nijar hukumomin kiwon lafiya sun bada sanarwar dakatar da tallafin kudaden tiyatar haifuwa da aka saba yiwa mata kyauta sakamakon wasu dalilai masu nasaba da tsarin aikin, amma kuma za a ci gaba da tsarin bada magani kyauta ga mata masu juna biyu da yara kanana.

Da yake karin bayani dangane da wannan sabon mataki na janye tallafin kudaden tiyatar mata a yayin haihuwa wato Cesarean ko C-Section, Ministan kiwon lafiya Dr. Iliassou Idi Mainassara ya ce abin na da nasaba da tsarin aikin projet PAPS wanda ya shafe shekara guda ya na daukar dawainiyar irin wannan aiki a matsayin na gwaji.

Ministan ya bada tabbacin cewa tsarin nan na bada magani kyauta ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar na nan daram haka kuma za a ci gaba da kula da mata masu juna biyu kyauta kamar yadda gwamnati ta kudirta wato gratuite des soins.

A ranar 31 ga watan nan na Disamba ne tallafin Projet PAPS ke zuwa karshe sai dai shugabar kungiyar ‘yan jarida masu kula da fannin kiwon lafiya Hajiya Amina Hachimou, na cewa janye tallafin tiyatar haihuwa a yanayin da mata ke ciki a yau a Nijar wani abu ne dake bukatar dogon nazari.

Ainihi gwamatin marigayi Tanja Mamadou ce ta bullo da tsarin bada magani kyauta ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar da haifuwa tare da daukar dawainiyar matan dake bukatar tiyatar haihuwa da nufin takaita yawan mata da yaran da ke rasuwa a lokacin nakuda ko kuma bayan haihuwa.

Haka kuma dukkan gwamnatoci da suka biyo baya sun ci gaba da mutunta wannan tsari, ko da yake abin na fuskantar tangarda saboda yadda wasu likitoci ke gaban kansu yayin da a wasu lokutan ake zargin gwamnati da rashin biyan bashin magungunan da asibitoci suka bayar a karkashin wannan tsari.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Lafiya A Nijar Sun Bayyana Shirin Janye Tallafin Tiyatar Haihuwa