A zantawa da wakilin Muryar Amurka a Kano, kwamishinan ‘yan sandan jihar Alhaji Sama’ila Dikko ya ce daga yanzu tilas ne sai kowane makiyayi ya nunawa jami’an tsaro takarda daga shugabanninsa ko kuma ofishin ‘yan sanda na yankin da ya fito kafin a bar shi ya yada zango a jihar Kano.
Daga shugabanninsu na Fulani ma in aka samu takardan ya wadatar, don takardan ce z tai nuna ina suka fito kuma ina za su.
Kuma a cikin takardan akan bayyana adadin dabbobin da kuma wanda ya mallaka.
Muryar Amurka ta kuma tambaye shi yaushe ƙa'idar za ta fara aiki, yayin da ya mana bayani cewa "mu a Kano so muke mu san baƙin daga ina suka fito, kuma ina za su, muna iya bakin ƙoƙari kan hakan. Mu tabbatar da cewa zaman lafiya ya samu."
"Batun matsuguni ma za mu sa masu ido mu tabbatar ba a samu matsala ba, da taimakon hakimai, dakatai da masu anguwanni."
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5