Hukumomin Jihar Kwara Sun Kaddamar Da Bincike Kan Yadda Aka Kona Wata Matashiya Har Lahira

Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq (Facebook/Gwamnatin Kwara)

Hukumomi a jihar Kwaran Najeriya na gudanar da bincike akan kisan wata yarinya mai suna Fatima Abdulkadir ‘yar kimanin shekaru 18 ta hanyar kona ta da wuta.

Wannan Al’amari dai da ya faru a kauyen Mushe Gada dake yankin karamar hukumar Kayama ya yi matukar tayar da hankalin mazauna Garin.

Bayanai dai sun nuna cewa wata matashiyar da suke aikin tsaron wani kantin magani ne tare da margayiyar mai suna Miraku ita ce ake zargin ta bankawa Fatiman wuta a daki a sakamakon wata rashin fahimtar juna da ta shiga tsakaninsu.

Malam Tajuddin Aliyu ya yi magana da yawun iyalan margayiya Fatima inda ya yi karin haske akan yadda lamarin ya faru da kuma matsayarsu. Ya ce yarinyar ta rufe kokofi wajen guda uku tun daga dakin da Fatima ta ke sannan ta zuba mai ta taga ta kunna wuta. Ya kuma ce gawar na asibitin Ilori.

Dan majalisar dokokin jihar Kwaran mai wakiltar karamar hukumar Kayama Hon. Sa’adu Baba Ahmed ya ce sun samu labarin aukuwar lamarin kuma har sun fara bin kadin batun domin tabbatar da adalci.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kwaran Mr. Ajayi Okasanmi ya shedawa manema labarai cewa ba shi da cikakken bayani akan lamarin saboda haka zaiyi bincike akai kafin yace wani abu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Jihar Kwara Sun Kaddamar Da Bincike Kan Yadda Aka Kona Wata Matashiya Har Lahira