Matakin da ake ganin zai taimaka wajen farfado da hada hada saboda haka wasu suka fara kiran mahukunta su fadada abin zuwa sauran sassan jihar.
Matakin wanda tuni ya fara aiki daga wannan laraba 6 ga watan Afrilun 2022 na hangen bai wa jama’ar da’irar Tilabery damar samun walwala a albarkacin watan azumin Ramadan kamar yadda za a ji Karin bayani daga bakin magajin gari Elhadi Moussa Douma.
Yace a wajejen karfe 7 na yamma ake buda baki a nan yankinmu alhali dokar hana zurga zurgar Babura kan fara aiki daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe saboda haka muka yanke shawarar dage wannan mataki zuwa 7 da rabi da nufin shafe hawayen al’uma dake korafi akan rashin samun sukuni a wannan lokaci.
Mazaunan garin Tilabery da kewaye sun yaba da wannan mataki ganin mahimmancin babura a rayuwar jama’a ta yau da kullum.
Sai dai mazaunan wasu daga cikin sassan jihar na ganin bukatar fadada wannan mataki dake zuwa a wani lokacin da dokar hana zurga zurgar Babura ta haddasa tsayawar al’amura cik inji wani mazaunin karkarar Makalondi Cyaman Arzika.
Editan jaridar la Roue de l’Histoire Ibrahim Moussa mai sharhi akan sha’anin tsaro wanne ya yaba da matakin samarda sassauci ga jama’r da’irar Tilabery ya gargadi hukumomi su yi taka-tsan-tsan da abubuwan dake kai da kawo.
Tsanantar aiyukan ta’addanci a jihar Tilabery mai makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso ya sa gwamnatin Nijer kafa dokar ta baci wace a wani bangarenta aka hana amfani da Babura yau shekaru a kalla 5.
Dage wannan mataki a karshen 2021 bai zo da kyaukyawan sakamako ba mafari kenan aka sake farfado da wannan doka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5