A jamhuriyar Nijar hukumar kula da kamfanonin wayar sadarwa ta ci tarar wasu kamfanonin wayar tafi da gidanka dubban milioyon CFA bayan zagayen da ma’aikatan hukumar suka gudanar a jihohin kasar ya gano laifuka da dama da suka saba yarjejeniyar da kamfanonin suka cimma da gwamnatin ta Nijer kafin ta ba su lasisin soma aiki.
A taron manema labaran da suka kira a ranar litinin 17 ga watan Yuli, shugabanin hukumar ARCEP sun fara ne da yin bayani game da binciken da jami’an hukumar suka gudanar a yankunan da jama’a suka koka da rashin ingancin layin wayar telephone a shekarar 2021.
Dukkan damammakin da hukumar ta ARCEP ta ce ta bai wa wadanan kamfanoni domin su gyara laifukan da suke aikatawa abin ya ci tura, mafarin da ya sa aka ci su tara kamar yadda dokokin Nijar suka yi tanadi.
Muryar Amurka ta tuntubi wani jami’i a Zamani com, Hashim Ali domin jin matsayin kamfanin game da wannan hukunci, sai dai bai daga wayarsa ba to amma jami’in kamfanin Niger Telecom Malam Talibi da muka zanta da shi ta waya ya bukaci a ba shi lokaci idan ya gama tattara bayanai zai waiwaye mu.
Saurari rahoton a s sauti :
Your browser doesn’t support HTML5