Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yiwuwar Kara Farashin Kiran Waya Da Shiga Yanar Gizo A Najeriya


Shugaban INEC Ya Gana Da Shugabani Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa
Shugaban INEC Ya Gana Da Shugabani Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta ce tana gudanar da wasu sauye-sauye a kan ayyukan gudanarwar kamfanonin sadarwa da kudaden da suke biya a kowacce shekara a kasar.

A cikin sauye-sauyen da hukumar ta NCC ke kan gudanarwa har da duba farashin ayyukan da kamfanonin sadarwa a kasar ke samarwa ga 'yan kasa.

Hukumar ta ce tana wadannan sauye-sauyen ne domin daidaita gudunmawar da ayyukan sadarwa ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin kasa don bin sahun takwarorin ta na kasashen duniya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin jawabin da shugaban hukumar ta NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ya yi, a lokacin wani taron jin ra’ayoyin ‘yan kasa da ya gudana a birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

Wasu majiyoyi daga hukumar sun yi nuni da cewa, da zarar NCC ta kammala aikin sauye-sauyen da ta ke kai a halin yanzu, akwai yiwuwar farashin kudin kira da na shiga yanar gizo su karu a kasar.

Wannan mataki na baya-bayan nan da hukumar sadarwa ta dauka na sauye-sauyen, ya ci karo da sanarwar yiyuwar raguwar farashin kiran waya da amfani da yanar gizo da kashi 65 cikin 100 da maitaimakin shugaban Najeriya ya sanar a ranar 25 ga watan Yuni a yayin wani taro.

Farfesa Yemi Osinbajo, a wancan lokacin ya bayyyana cewa gwamnati na wani gaggarumin aiki na tabbatar da rage farashin shiga yanar gizo a kasar, shirin da ya ce zai rage farashin kowanne gigabait daya da kusan kashi 70 cikin 100, ta yadda farashin ba zai wuce naira 390 ba nan da shekara 3 masu zuwa, domin saukaka shiga yanar gizo ga 'yan kasar.

Masani kan sha'anin fasahar zamani da kuma yanar gizo, Yusufudeen A. Yusuf, ya ce wannan rashin daidaito a tsakanin bangarorin gwamnati na cimma matsaya a kan ababen da suka shafi kasa ba abu ne mai kyau ba, inda ya yi kira ga gwamnatin kasar ta hada kai domin cimma nasara a ayyukan ci gaban kasa.

Duk kokarin jin karin bayani game da wannan lamarin daga bakin hukumar NCC ya ci tura bayan taron.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG