Barrister Emmanuel Sublim ya shaida hakan ne a wani taro na wuni guda akan batutuwan da suda shafi mata, zaman lafiya da kuma tsaro a Najeriya, wanda kungiyar mata ta Majalisar Dinkin Duniya ta Gudanar tare da Gwamnatin kasar Norway daya gudana a Bauchi.
A cewar Sublim, iyayen wadanda aka yi wa ayyukan ashan, na kin yin bayani wa kotuna game da laifin da aka aikata akan ‘ya’yan nasu wanda hakan yana kawo cikas ga ayyukan kotuna wajen gabatar da wanda ake zargi da aikata laifin.
Babban Magatakardan ya kara da cewa wani abin bakin ciki shi ne, yawancin irin wadannan batutuwa ba sa tsayawa kan tabbatar da zargi sabili da matsalolin bincike ko kuma tabbatar da zargi ko kuma a yayin da aka tura batun ma’aikatar shara’a don bada shawara.
Ya kuma ce rashin sa’ar shi ne, rashin wadanda za su iya bin diddigin abin dake faruwa daga lokacin da aka kama wani da ake zargi har zuwa lokacin da aka kai kotu.
A nata jawabin Darekta a Ma’aikatar Mata a jihar Bauchi Madam Esther Patrick ta bukaci ganin ana tafiyar da mata a shirin gudanar da batutuwan zaman lafiya da tsaro domin ganin zahiri yadda zai shafi rayuwar mata.
Akan batun da ma’aikatar mata ke yi Madam Esther, ta ce akwai kwararru da kungiyar UNFPA ke kokarin ganin duk matsalolin dake da nasaba da cin zarafin mata an tabbatar da an nemi an hukunta duk wanda yaci zarafin ‘ya mace.
Mrs. Beatrice Gondi ta Kungiyar Mata ‘yan jarida dake yakar cin zarafin mata, ta bukaci iyaye su bada goyon baya wa mahukunta domin magance wannan mummunan aiki da ake tabkawa a cikin al’umma.