Daya daga cikin lauyoyin da ke kare shugabannin kungiyoyin fararen hula da gwamnatin Nijar ta kame a ranar lahadin da ta gabata yayin wata tarzoma da ta barke a titunan Yamai a kan batun tsarin kasafin kudaden kasar da ke shan suka, ya bayyana rashin jin dadinsu akan lamarin.
Bayan da ya saurari 'yan gwagwarmaya alkali mai bincike ya zargesu da laifin gudanar da zanga-zanga ba da izinin hukuma ba, saboda haka ya bada ajiyarsu a gidajen yari dabam-dabam kafin a waiwayesu a wata ranar da ba a bayyana ba, matakin da lauyoyin da ke karesu ke gani tamkar tsararriyar da aka kitsa takanas.
A kokarin jin ta bakin alkalin da ke kula da wannan shari'a ko lauyoyin da ke kara da sunan gwamnati, wakilan muryar Amurka sun ci karo da jami'an tgsaron da ke binciken id card a bakin kotun, inda suka ce an hana yan jarida shiga farfajiyar kotun.
Tururuwar jama'a ne suka hallara a kofar kotun ta birnin Yamai domin bawa wadannan shugabannin kungiyoyin kare hakkin dan adam goyon baya.
A ranar lahadin da ta gabata ne hukumomi suka kama wadannan jami'an fafutuka tare da wasu matasa da aka kiyasta cewwa sun kai 23 lokacin da hatsaniya ta barke a titunan Yamai da nufin gwadawa mahukunta bacin rai akan matakinsu na hana gudanar da jerin gwano da zaman dirshan a ci gaba da watsi da dokar harajin shekarar 2018.