Hukumomi A Najeriya Sun Musunta Bullar Shan-Inna A Kudu

Dakta Emmanuel Odu Mukaddashin Daraktan Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotanni dake cewa an samu bullar cutar Polio ko kuma a shan-inna a kudu maso kudancin kasar, bayan da aka haifi wani yaro da nakasa a jikinsa.

Mukaddashin daraktan hukumar kula da lafiya matakin farko ta Najeriya, Dakta Emanuel Odu, yace suna nan tsaye don ‘daukin gaggawa ga duk labarin da suka samu na bullar shan-inna a dukkan sashen Najeriya, baya ga rigakafin gida-gida da suke yi.

Labarin bullar cutar shan-inna a jihar Cross Rivers, ya sanya zulumi ga al’ummar yankin kasancewar ya zamanto wani abu da ba a taba gani ba. hakan yasa jami’an yaki da shan-inna garzayawa jihar, inda suka gwada yaron da lamarin ya shafa su gano sawayensa sun tankwashe saboda tawaya da ya samu kafin a haife shi.

A cewar babban jami’in na kiwon lafiya, hukumar ta mayar da hankali ne wajen kula da yankunan da aka kwato daga Boko Haram, da samun bullar cutar a bara ya mayar da hannun agogo baya daga fitar da Najeriya a matakin karshe daga kasashe masu shan-inna a Duniya.

Domin karin bayani saurari rahotan nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomi A Najeriya Sun Musunta Bullar Shan-Inna A Kudu - 2'34"