Hukumomin Italiya su na ci gaba da auna barnar da ta wakana a tsakiyar Norcia, kwana guda a bayan da wata girgizar mai karfin awu 6 da kimanin rabi ta abku a garin.
Ba a yi hasarar rai a wannan girgizar kasa ta jiya lahadi ba, duk da cewa karfinta ya zarce na wadda ta faru ranar 24 ga watan Agusta har ta kashe mutane kimanin 300. Amma girgizar ta yi barna sosai.
A Norcia, girgizar kasar ta lalata wasu majami’u da dama, ciki har da Majami’ar Basiliza of St. Benedict da aka gina tun karni na 14 a wurin da aka haifi St. Benedict mutumin da ya kafa darikar nan ta Benedictine; da kuma wata majami’a mai suna Cathedral of St. Mary Argentea wadda ta yi suna wajen wasu zane-zanen karni na 15.
Har ila yau girgizar kasar ta jiya lahadi ta rsuhe majami’ar San Francesco wadda ‘yan darikar Francisca suka gina a karni na 14. A baya an sake gina wannan majami’ar bayan wata girgizar kasar da ta rushe ta a shekarar 1859.
Wasu sassan ganuwar da Rumawa suka gina a Norcia, wadanda suka lalace a girgizar kasa a baya, sun rushe har kasa a girgizar ta jiya tare da hasumiya da yawa.
Kwararru sun ce girgizar kasar ta jiya lahadi it ace mafi karfi da aka gani a yankin tun wata mai karfin kusan awu 7 da ta kashe mutane dubu biyu da dari bakwai da talatinm da biyar a kudancin Italiya a shekarar 1980.