‘Yan bindigar sun kai harin ne lokacin da jami’an tsaron ke gudanar da ayyukansu a yankin karamar hukumar Dambua dake jihar Borno. A cewar wata sanarwa da jami’in riko na rundunar sojan Najeriya kanal Sani Usman Kuka Sheka ya aikawa manema labarai, yace sun kai sumame ne a wasu kauyuka biyu da ake kira Talala da Ajigir dake kudancin jihar Borno.
A lokacin da jami’an ke kan hanyar su ta dawowa ne maharan suka kai musu hari a kauyen Yugundari, har suka hallaka jami’an soja 5 suka da ‘Yan Banga guda Uku da kuma Civilian JTF guda ‘Daya, haka kuma sun raunata wasu jami’an soja 19, wanda kuma yanzu haka suke karbar magani.
Sanarwar tace rundunar ta samu nasarar lalata daya daga cikin manyan motocin ‘yan ta’addan da kuma kwato wasu bindigogi biyu da ake kira anti air craft, wadanda ke harbor jiragen sama da sauran wasu makamai masu yawa a moboyar ‘yan ta’adan. Sai dai sanarwa bata bayyana kame ko kuma hallaka ko mutum ‘daya daga cikin maharan ba.
A wata sanarwar ta daban kuma dake dauke da sa hannun Kanal Usman Kuka Sheka, na nuni da cewa rundunar ta samu nasarar kame wani mutun da ake zargi da cewa shine ke aikawa ‘yan Boko Haram magunguna da kuma kwayoyi, a tsakanin kauyen Firgi da Zawan dake a karamar hukumar Bama a jihar Borno.
An dai kame wannan mutum ne a lokacin da yake kokarin shiga dajin Sambisa jiya Lahadi, rundunar tace ta kame wani mutum mai shekaru 35 ne kawai yayin da sauran suka arce zuwa cikin Daji, haka kuma sun gano magunguna da suka hada da garin Glucose da maganin rade radin ciwo da sauran wasu magunguna da yawa, yanzu haka dai runduanar tana ci gaba da bincike akan mutumin da aka kama. Sanarwar ta kara da cewa sun kama wani da ake zargin cewa shine ke kaiwa ‘yan Boko Haram Man Fetur, da ake kira Fantoma Lasani, wanda ake kame da hadin gwiwar jami’an tsaron farin kaya a tashar Muna lokacin da yake kokarin shigowa don daukar matarsa.
Shi dai wannan mutumin da ake zarga ya fito ne daga kauyen Filatari karamar hukumar Bama a jihar Borno, kuma yana daya daga cikin masu rashin kishin kasa saboda an gano cewa yana aikawa yana daya daga cikin masu aikawa ‘yan Boko Haram Man Fetur da kuma Gas, a tsakanin yankin Bama da Goza wadanda dukkanninsu ke tsakanin dajin Sambisa.
A jiya Lahadi, jami’an tsaro sun bindige wani dan kunar bankin wake a unguwar da ake kira Rambuwa Road, inda yayi kokarin kutsawa cikin jama’a har jami’an suka bude masa wuta ya kuma tashi da ‘dan kunar bakin waken, sai dai babu wanda ya samu rauni.
A yan kwanakin nan dai ana samun hare haren kunar bakin wake da kuma kwantan bauna, wanda jami’an tsaro ke kira ga jama’a da a dunga mayar da hankali game da abubuwan da ke kewaye da su da kuma mutanen da ke shigowa.
Domin karin bayani.