Hukumomi a tsibirin Bali dake Indonesia, sun ba da kololuwar gargadin yiwuwar fuskantar aman wuta daga tsaunin Agung, wanda yake ci gaba da tumbidin toka da hayaki.
Dutsen ya na ci gaba da amayo laka da narkakken dutse wanda ke sakkowa kasa ta jikinsa.
Jami'ai sun fadada yanki dake da mutukar hatsari zuwa kilometer 10 daga jikin wannan dutse, matakin da yake nufin cewa mutane dubu dari dake kusa da wannan dutse mai aman wuta, za su fice daga gidajen su.
Kakakin hukunmar ayyukan gaggawa ta kasar ya gargadi mutane cewar narkakken dutse da ke fitowa daga wannan dutse zai mamaye wuraren da suke kasan wannan dutsen.
Jami’ai sun ce an ji karar fashewar da wannan dutse mai aman wuta ya yi daga wurare masu nisa, yayin da aka ga wuta na fita daga samansa.
Toka daga aman dutsen ta tursasawa jami’ai da su rufe filin saukar jirgin sama na yankin a safiyar ranar litinin, inda aka soke jirage 445, lamarin da ya yi sanadiyar shafar tafiyar mutane dubu hamsin da tara.