Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zabe Na Farko Yau A Kasar Nepal


Niger Elections
Niger Elections

Yau lahadi 'yan kasar Nepal ke jefa kuria, a zaben farko da ake gudanarwa a kasar, kuma an tsara zaben gida biyu ne, wanda ake fatar ganin jamaa masu jefa kuria sun fito kwansu da kwarkwatar su.

Yau ne ake jefa kuria a NEPAL domin zaben sabbin shugabannin majilisar dokokin kasar da suka hada da ‘yan majilisar sabbin jihohi 7, da kuma yan majilisar dokokin tarayya.

Wannan dai shine zaben farko da aka gudanar a kasar.

Su dai wadannan da za a zaba sune zasu samar da shugabannin gundumomin su,musammam jihohi kana sune zasu samar da dokokin da za ayi anfani dasu wajen tafiyar da shugabannin nasu.

Ana sa ran masu jefa kuriar na yau su fito da yawan gaske a zaben da aka kasa gida biyu.

Sama da mutane miliyan 3 ne dai ake sa ran su fito daga arewacin kasar kawai, ciki ko har da yankin nan da ya fuskanci matsalar girgizar kasa shekaru biyu da suka gabata.

Suko yankin kudancin kasar da suka fi yawan jamaa zasu gudanar da nasu zaben ne a ranar 7 ga watan gobe.

Nepal dai ta dan jima da kasancewa cikin matsuwa domin ta gudanar da mulkin demokaradiyya, musammam tun lokacin da masu zanga-zanga suka matsawa tsarin mulkin sarauta ya kauce daga shekarar 2006.

Ba a dai tabbatar da sahihancin dokar kasar ba har sai zuwa shekarar 2015 bayan anta samun gutsri tsoma tsakanin jamiyyun siyasa.

Abin da dai ake fata shine aga, cewa sabuwar gwamnatin ta demokaradiyya ta kawo gwamnatin kasar kusa da jamaa, wadda tana daya daga cikin kasashen duniya da take sahun gaba a talauci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG