Ministan shari'a na kasar Pakistan ya yi murabus daga mukaminsa makwanni uku bayan da kungiyoyin addinin Islama suka yi ta bore. Zanga Zangar ta sa an rufe titunan da ke hada babban birnin kasar da sauran garuruwa a Pakistan.
Hakan ya yi sanadiyyar zama tarzoma a ranar Asabar yayin da ‘yan sanda suka yi kokarin tarwatsa tarin zanga zangar, inda jami’an tsaro 100 da masu bore dama suka ji raunuka.
Masu zanga zangar wadanda ke wakiltar kungiyoyin addinin Islama daban-daban suna so ne ministan shari'a Zahid Hamid, ya yi murabus bayan wani dan chanji da aka yi a dokokin zaben kasar, wanda suka ce ya sabawa addininsu.
Gwamnatin kuma ta shaida musu cewa gyaran da aka yi tangarda aka samu daga ma'aikata an kuma gyara shi. Mai magana da yawun kungiyoyin Threek E Labaik Ejaz Ashrafi, ya bayyana cewa babbar bukatar su ta biya.
Masu zanga zangar sun dakatar da harkokin yau da kullum a babban birnin kuma akalla mutane biyu har da yaro sun rasa rayukansu bayan da motocin daukan marasa lafiya da suke ciki suka kasa kai wa ga asibiti akan lokaci.
Facebook Forum