Hukumar Tattara Kudaden shiga ta Kasa da rarraba su shiyya shiyya, har kananan hukumomi ta RMAFC ta musanta rahotanni da ke cewa ta amince da yi wa wasu manyan jami'an gwamnatin karin albashi.
A baya-bayan nan rahotanni sun yi nuni da cewa an karawa shugaban Najeriya, mataimakinsa da manyan 'yan siyasa albashi.
Sai dai yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, shugaban hukumar, Mohammed Bello Shehu, ya musanta rahotonnin da wasu kafafen yada labarai suka buga kan wannan batu.
A cewar Mohammed, hukumar ba ta samu wani umurni na kara wa manyan ma'aikatan gwamnati albashi a yanzu ba, sai zuwa gaba kadan.
Ita dai hukumar wacce ake kira Revenue Mobilisation and Fiscal Commission, ta ce da zarar ta samu wannan umurni, za ta sanar da 'yan Najeriya.
Ga yadda hirarsu ta kasance da wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5