Hukumar Zaben Nijar Ta Shiryawa 'Yan Takarar Shugaban Kasa Muhawara

A ci gaba da tsaren-tsaren zabubbukan da za a gudanar a watan nan na Disamba a Jamhuriyar Nijer, hukumar zabe ta CENI ta shirya wata mahawarar bainar jama’a domin daliban tsangayar kimiyar ilimin doka a jami’ar Abdoulmoumouni da ke birnin Yamai, babban birnin kasar.

Muhimmancin gudunmawar matasa wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe ya sa hukumar zabe ta CENI shirya mahawarar a bainar jama’a domin jan hankulan daliban tsangayar kimiyar ilimin doka ta jami’ar Yamai, don ganin sun kaucewa fadawa tarkon ‘yan siyasa musamman irin wannan lokaci da ake gab da gudanar da babban zaben, a cewar kakakin hukumar zabe Nafiou Wada ya shaida.

A wani abin da ke zama sabon tsari a tarihin zabubbukan Nijar, akasarin ‘yan takarar zaben shugaban kasa sun ziyarci jami’ar Yamai a wannan karon, a bisa gayyatar kungiyar dalibai ta UENUN, inda kowanne daga cikinsu ya yi wa dalibai bayani a game da ayyukan da yake sa ran yi wa kasa idan ya samu nasarar lashe zaben na ranar 27 ga watan disamba.

Dalili kenan da ya sa hukumar zabe ta ga dacewar yi wa dalibai hannunka mai sanda.

Baya ga batun zaman lafiya, wannan mahawara na hangen ganar da matasa hikimomi da dubarun tsara zabe a doka.

Mahamadou Hachimou shi ne babban magatakardan kungiyar UENUN daliban jami’ar Yamai ya ce, wannan tsare-tsare abu ne mai kyau ga dimokradiyyar Nijer.

Fiye da kashi 50 daga cikin 100 na mutum million 7.5 da suka yi rajistar zabe a Nijar, matasa ne.

Yayin da bayanai ke nunin ‘yan siyasa kan yi amfani da matasa don cimma burinsu a siyasa, ba tare da la’akkari da abubuwan da ka iya tasowa ba, saboda haka kenan kungiyoyi da hukumomin Nijer ke jan hankalin matasa su yi karatun ta nutsu.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zaben Nijar Ta Shiryawa 'Yan Takarar Shugaban Kasa Muhawara