Tsarin tattara sakamakon zabe daga yankunan karkara zuwa rassan hukumar zabe na jihohi, zuwa cibiyar hukumar da ke birnin Yamai, tare samfarin kuri’un da za a yi amfani da su a yayin zaben kananan hukumomi na ranar 13 ga watan Disamba, na daga cikin mahimman batutuwan da shugabanin hukumar CENI suka yi wa ‘yan siyasa bayani akansu a yayin ganawar, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar Dr. Aladoua Amada ya yi karin bayani akai.
Abdoulaziz Agali na jam’iyar Alhali ya ce, sun gamsu da ka’idodin da hukumar ta CENI ta zo da su, kuma sun shirya tsaf domin gudanar da zaben.
Sai dai ra’ayoyi sun sha banban a tsakanin ‘yan siyasa. Wakilin jam’iyar PSD Bassira Abdoulkader Mohamed ya ce, akwai alamar daurin kai game da wasu daga cikin ka’idodin da hukumar ta CENI ta zo da su.
Za a ci gaba da bai wa ‘yan kasa damar karbar katunan zabe har zuwa ranar 7 ga watan Disamba, amma hukumar CENI ta ce, dukkan wadanda suka makara na da damar karbar nasu katunan a runfunan zabe a ranar da za a kada kuri’a.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5