Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajistan 'Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje

Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajitan ‘Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje

Hukumar zaben kasar Nijar ta fara gudanar da rajistar ‘yan kasar dake zama a kasashen waje, don gudanar da zaben wakilai guda biyar da zasu wakilci al’ummar kasar Nijar dake zama a ketare.

PLATEAU, NIGERIA - Kimanin ‘yan kasar Nijar dubu goma ne ke zaune a Jihar Filato. Alhaji Ahmad Zakariyya Suleiman, shugaban kungiyar ‘yan Nijar mazauna Jihar ta Filato ya ce sun fadakar da al'ummarsu, don su fito yin rajistar.

Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajitan ‘Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje

Muhammad Danladi Suleiman, babban jami’in tsaro na kungiyar a Jihar Filato, ya ce kasashen duniya goma sha biyar ne zasu zabi wakilai biyar da zasu wakilci al’ummar Nijar dake zama a wasu kasashe.

Sakataren yada labarai na kungiyar, Alhaji Muhammadu Usman shi kuma ya ce aikin rajistar na tafiya yadda ya kamata, sai dai na’urar yin rajistar basu wadatar ba.

Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajitan ‘Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje

Wasu da suka yi rajistar, sun bayyana fatan wadanda nan gaba za a zaba, zasu inganta tattalin arzikin jama’a, ilimi, ayyukan yi da sauransu.

Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajitan ‘Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje

Jami’in hukumar zaben kasar Nijar dake gudanar da rajistar, Ibrahim Sale Kankani ya ce kwanaki goma sha biyar da hukumar ta kebe don yin rajistan, sun kasa.

Al’ummar Nijar mazauna Najeriyan dai suka ce suna bin dokokin da hukumomin Najeriya suka gindaya musu, don tabbatar da al’ummarsu basu shiga matsala ba.

Saurari cikakken rahoton daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zaben Nijar Ta Fara Gudanar Da Rajitan ‘Yan Kasar Dake Zama Kasashen Waje.mp3