Karkashin wani tsari na musamman da hukumar zaben ta INEC ta bullo dashi, ta shirya gangamin wayar da kan dalibai a daya daga cikin jami’o’in dake kowace shiya a shiyyoyi 6 na fadin Nigeria.
A shiyyar arewa maso yamma, dai hukumar ta INEC ta zabi Jami’ar Bayero dake Kano, inda aka gudanar da gangami tare da gabatar da lacca daga masana da kuma jami’an hukumar ta INEC.
Malam Garba Lawan shine Jami’in hulda da jama’a na ofishin hukumar a nan Kano. Ya ce a ci gaba da kokarin da hukumar ta keyi domin ta wayar wa matasa kai mahimmancin harkar zabe domin su zabi mutane kwarai, su fito su yi takara. Lallai ne su yi rajista kana su jefa kuri’a saboda matasa su ne suka fi yawa. An yi kira ga matasa da su kiyayi shiga bangar siyasa a kowane mataki.
Dalibai maza da mata da suke karatu a fannoni dabam dabam a jami’ar ta Bayero ne suka halarci gangamin. Ibrahim Muhammad Abubakar wani dalibi ne y ace ya koyi abubuwa da yawa da bai sani ba. Wata daliba, mai suna Maryam cewa ta yi an wayar musu da kai akan zaben mutane na gari ba wadanda zasu bata kasar ba. Haka kuma sun fahimci ‘yancin su da anfanin mallakar katin zabe.
Kodayake hukumar zaben ta INEC ta shafe fiye da shekara guda tana aikin bada katin zaben a hedkwatar kananan hukumomin Nigeria, amma har yanzu akwai mutane da dama da ba su kai ga samun katin zaben ba. Daya daga cikin daliban da suka halarci gangamin na cewa wasu bas u da karfin gwuiwar karban katin zabe saboda suna tunanen ko sun yi zaben ba za’a basu abun da suka zaba ba.To amma saboda wanna wayar da kai an zaburar da mutane.
Ranar 17 ga wannan wata na Agusta ita ce ranar kammala aikin ba da katin zaben ga ‘yan Nigeria da suka cancanta.
A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari don jin karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5