Kungiyar al'ummar Kudancin Borno, a karkashin shugabancin Injiniya Ibrahim Usman, ta fito tana cewa lokaci ya yi da yakamata kujerar gwamnan jihar ta fada hannun dan kudancin jihar a karon farko cikin shekaru fiye da 16 da ake mulkin dimokradiya a Nigeria.
Da yake magana a taron da manema labarai, Injiniya Usman yace dalilin daukar matakin shine su shaidawa mutane cewa zasu yi taron shugabannin kudancin jihar, inda zasu zaburar da mutanensu su tashi tsaye a wannan lokacin da zabe ke karatowa. Su ma su nemi dan yankin ya zama gwamnan jihar ba wai kullum su dinga hakura da matsayin mataimakin gwamnan ba. Saboda haka wai sun tattauna da al'ummomin Borno ta Tsakiya da na Arewacin Bornon akan wannan bukatarsu. Wasun su sun gane bukatar a rika damawa da al'ummar Kudancin Borno ta wajen bin tsarin karba-karba na mukamin gwamnan jihar. Idan anan neman zaman lafiya dole a nemi adalci, inji Injiniya Usman.
Akan ko kudancin Bornon nada mutane da za su iya tsayawa takara, Injiniya Ibrahim Usman ya ce idan lokacin ya yi zasu fito.
Masu hannu da shuni a yankin sun amince su taimakawa duk dan takarar da ya fito neman gwamna.
A saurari firar da Haruna Dauda ya yi da Shugaban Kudancin Bornon
Facebook Forum