Hukumar Zabe a Najeriya tace za’a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarraya ranar Asabar, sha shida ga watan Fabrairu na shekara ta dubu biyu da goma sha tara, sannan a gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi, da na tarayya a ranar biyu ga watan Maris.
Wannan ne karo na farko a tarihin Nigeria da hukumar zabe a Najeriya zata fitar da jadawalin zabe shekara daya kafin a yi zaben. Hukumar kuma ta bada tabbacin cewa, daga yanzu za a rika gudanar da zabukan ne a ranakun da aka ambata, ba tare da dagawa ko jinkirtawa ba.
Sai dai batun zaben fidda gwani da hukumar zabe tace za a gudanar, da warware korafe korafe da zasu biyo bayansu da za a yi a watan Agusta na shekara ta dubu biyu da goma sha takwas, ya haifar da kace nace tsakanin ‘yan siyasa.
Da yake tsokaci dangane da batun, tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Bauchi Shu’aibu Abubakar, wanda dan jam’iyar APC ne, ya bayyana cewa, hukumar zabe zata yi riga mallam-massalaci idan bata canza tsarin, ta maido shi kamar yadda aka saba gudanar da shi ba.
To amma a nashi bayanin, Dr Umar Ardo na jam’iyar PDP, ya bayyana goyon bayansa ga matakan da hukumar zaben ta dauka tun daga rajistar sababbin jam’iyu har zuwa fitar da jaddawalin.
Ga cikakken rahoton da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda ta aiko daga Abuja: