Tuni dai babbar jam'iyyar adawa ta APC tayi barazanar zata kai hukumar 'Yansanda ta farin kaya watau SSS gaban kotu, domin kutsawa data yi cikin ofishin adana bayanai na jam'iyyar dake Legas. APC tana cewa tilas hukumar ta sami izinin kotu kamin ta dauki irin wannan mataki.
Ita dai hukumar 'Yansanda ta farin kaya da ake kira SSS ta dira kan ofishin jam'iyyar ce a Ikko kan zargin cewa APC na kokarin buga katunan rijistar masu zabe na bogi.
Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya tana zargin jam'iyyar hamayyar da cewa tana kokarin murde zaben kasa mai zuwa. Jam'iyyar tana zargin cewa APC ta kafa irin wadannan ofisoshi a duk jihohin Najeriya 36.
Amma da yake magana kan kai komo tsakanin jam'iyun biyu kan batun katin rijistar, kan ko ana iya buga na bogi, mukaddashin darektan hulda da jama'a na hukumar Mr. Nick Dazan, yace hukumar bata da wani fargabar cewa ana iya buga katunan rijista na bogi, domin ta yi tanadin da babu hali a yi haka.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5