A kudu maso yammacin Najeriya, jama’a sun bayyana mamakinsu ga irin rawar da jami’an tsaro suka taka a wajen wannan badakala.
Jama’ar Jihar Oyo sun nemi shugaba Goodluck Jonathan yayi gaggawar sauka daga karagar mulki.
Mallam Umaru Ja’e, cewa yayi “gaskiya abunda anka aikata baiyi daidai ba, masu bada doka da kansu, a ce suma an hana su zama.”
Shi kuwa Alhaji Issuhu Abubakar cewa yayi “wannan abun kunya ne a duk duniya, ba ma a Najeriya kadai ba, saboda haka, yanzu gwamnatin Najeriya, shi Jonathan ya kamata ya sauka. Wannan abun kunya, duk duniya.”
Amma ga Mallam Kyari Ali Bukar, harbawa ‘yan majalisar barkonon tsohuwa, da rufe kofofin majalisar abun nazari ne ga shuwagabanni a Najeriya.
“Gaskiya fisa billiLahi abunda ‘yan sanda suka yi, ba dai-dai bane, ba shine doka ba, amma kuma yayi haka, da akayi musu. Saboda su ‘yan majalisa da kansu, akwai matsala a tare da su. Ana kashe mutane, suna ji kullum, kuma sune doka, sun san da wannan abun. Aka kyale, har gashi ya kai ya kawo ana saka borkono a idanunsu.”