Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC), ta ce ta kintsa tsaf don gudanar da zabe a watan gobe a fadin Nijeriya, ciki har da inda ake fama da rikice-rikice, saboda za a yi amfani da irin dabarun da aka yi amfani da su aka gudanar da zabuka a kasashe masu fama da rikice-rikice.
A hirarsu da wakiliyarmu a Abuja, Madina Dauda mai magana da yawun hukumar zabe Nick Dazan ya ma yi kira ga kowani dan Nijeriya da ya tabbar ya mallaki kati kafin karshen wannan wata. Ya ce kafin hutun Kirsimeti da sabbuwar shekara, an kafa wani kwamitin duba yadda za a yi wadanda su ka gudu daga garuruwansu ko jihohinsu sanadiyyar tashe-tashen hankula sun sami sukunin kada kuri’unsu. Y ace yau ne ma kwamitin zai ba da rahotonsa.
Ya ce tun kafin kafa wannan kwamiti ma hukumar zabe ta gayyaci kwararru da masana don su ba da shawara kan yadda za a iya gudanar da zabe a wuraren da ake da tashe-tashen hankula ko kuma mazauna wuraren su ka gudu saboda tashe-tashen hankulan. Y ace wannan kwamiti zai yi nazarin shawarwarin da su ka bayar sannan ya kuma dubi yadda zai kwaskare su su dace da yanayin Nijeriya sumamman ma wuraren da ake fama da tashe-tashen hankulan. Ya ce akwai kuma wasu na’urorin da su ka lalace, kuma akwai wasu mutanen da katunansu su ka lalace ko su ka bata sanadiyyar dalilai dabandaban amma duk da haka an yi rajista ma mutane a kalla miliyan goma, wadanda idan Allah ya yadda za su sami katunansu kafin karshen wannan watan.
Your browser doesn’t support HTML5