Hukumar Yaki da Cutar kanjamau a jihar Maradi ta fadakar da matasa

Wata mai dauke da kanjamau

Hukumar yaki da cutar kanjamau ta jihar Maradi ta yiwa matasa matashiya dangane da illar cutar

Hukumar yaki da cutar kanjamau ko kuma sida ta jihar Maradi a jamhuriyar Niger, ta yiwa al’umma musamman ma matasa matashiya dangane da yaduwar cutar kanjamau.

Shugaban hukumar docta Alisumani Yaro ya bayyana cewa, an sami sama da mutane dubu shida dake fama da cutar kanjamau a jihar Marada cikin shekaru bakwai, wadanda daga cikinsu mutane dubu daya da dari tara da arba’in da daya ne kadai suke zuwa ganin likita domin shan magani.

Ya bayyana takaicin yadda sauran wadanda ke fama da wannan cuta suke kin zuwa neman magani duk da yake ana bada maganin ne kyauta, abinda ke haifar da yawan mace mace tsakanin masu kamuwar da cutar.

Likitocin sun bayyana cewa, an fi samun masu dauke da wannan cutar tsakanin mata da kananan yara wadanda basu da ‘yancin zuwa ganin likita da kashin kansu.

Wadansu matasa da Muryar Amurka tayi hira da su, sun bayana cewa gudun kada a kyamace su yasa mutane basu zuwa jinya ko sun san suna dauke da cutar.