Ministan lafiya na Najeriya Frofesa Onyebuchi Chukwu yace Najeriya tayi asarar kimanin naira Biliyan 132 ta dalilin illar zazzabin cizon sauro.
Ministan ya kuma bayyana cewa, zazzabin cizon sauro ne sanadin mutuwar kashi daya bisa uku na kanannan yara a Najeriya inda sama da mutane dubu dari uku suke mutuwa kowacce shekara. Bisa ga cewar ministan kashi 70% na mata masu juna biyu suna kamuwa da zazzabin cizon sauro, yayinda kashi 11% na mata masu juna biyu da suka rasa rayukansu, suna mutuwa ne ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro.
Wannan kiyasin inji shi, ya nuna irin hadari da barazanar da zazzabin cizon sauro yake da shi ga Najeriya. Ya kuma bayyana cewa, kasar na nesa da shawo kan cutar, duk da shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da ta kaddamar da ya hada da raba gidajen sauro da aka jika a magani domin rage kaifin cizon sauro.
Frofesa Chukwu yace tilas ne gwamnocin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi su nemi hanyoyin shawo kan cutar, yace za a iya cimma burin ne ta wajen hada hannu tsakanin gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu a cikin gida da kuma kasashen ketare.
Bisa ga cewarshi, zai zama dole gwamnati ta kara kason kudin da take kashewa a yaki da cutar, a kuma maida hankali kan cibiyoyi da ayyukan da ke taimakawa wajen shawo kan cutar, yayinda za a fadada aikin samar da gidajen sauro da aka jika a magani musamman a yankunan karkara.
Ministan ya kuma bayyana cewa, za a bukaci hadin kai da goyon bayan a’umma wajen cimma nasarar wannan yunkurin, wadanda suke da hakin tsabtace muhallansu da kuma kawar da matattarun ruwan da sauro ke yaduwa.