Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun UNICEF ya dauki matakin rage mace macen mata masu juna biyu da kananan yara a Najeriya


Wata mai jinya tana jawabi ga mata masu juna biyu
Wata mai jinya tana jawabi ga mata masu juna biyu

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya dauki nauyin wani shirin lafiya da nufin rage mace macen mata masu juna biyu da kananan yara a jihohin arewacin Najeriya goma


Asun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya dauki nauyin wani shirin lafiya da nufin rage mace macen mata masu juna biyu da kananan yara a jihohin arewacin Najeriya goma. Jihohin sune Bauchi, Kano, Jigawa, Adamawa, Borno, Nassarawa, Plateau Taraba, Yobe da kuma Gombe.

Shirin ya kunshi raba wadansu magunguna da kuma gidan sauro kyauta ga kananan yara da kuma mata masu juna biyu da nufin rage yawan mace macen mata masu juna biyu da kananan yara. Magungunan da aka raba yayin gudanar da shirin sun hada da sinadarin Vitamin A shudi da kuma Vitamin A ja, da maganin tsutsar ciki da ake kira Alberdozole, da kuma maganin rigakafin Zazazabin cizon sauro da kuma gidajen sauro.

Dubban mata masu juna biyu da kananan yara ne suka amfana da shirin da aka gudanar a jihohin goma na tsawon mako guda. Asusun UNICEF ya gudanar da shirin ne a yunkurin mara bayan cibiyoyin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu na shawo kan matsalolin lafiya makamantan haka da nufin rage mace macen dake da alaka da juna biyu da kuma kara azama a wannan yunkurin da bincike ya nuna ana bukatar daukar tsauraran matakai idan ana so a cimma wannan burin.

Asusun UNICEF ya da bada karfi a jihohin arewacin Najeriya kasancewa a shiyar ne aka fi samun mace macen a Najeriya. Bincike na nuni da cewa, yayinda kimanin mata dari biyar daga cikin dubu dari ke mutuwa lokacin haihuwa a kudancin Najeriya, kimanin dubu daya da dari biyu ke mutuwa daga cikin dubu goma lokacin haihuwa a arewa. Banda haka kuma adadin matan da ke fama da matsalar yoyon futsari yana karuwa.

Wata mai jego wadda take da yara shida, Hajara Aminu daya daga cikin matan da suka amfana da shirin daga kauyen Chinkilawa a karamar hukumar Warawa ta jihar Kano ta bayyana cewa, tana fafiyar kilomita bakwai kafin ta isa cibiyar jinya da suke zuwa awo. Ta bayyana cewa, tayi doguwar nakuda lokacin haihuwa kafin bayan lokaci mai tsawo aka dauketa a kan keke zuwa inda zata sami taimakon asibiti.

Bincike na nuni da cewa rashin samun isassar kulawa da jinya shine kan gaba daga cikin matsalolin dake haddasa mutuwar mata masu juna biyu a kasashe masu tasowa.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG