Yayin da tawagar ‘yan wasan Koriya ta Kudu ta bayyana a cikin jirgin ruwa daga ta kogin Seine a babban birnin na Faransa, an gabatar da su da su a matsayin ‘yan Jamhuriyar Dimokiradiyyar Koriya (Koriya ta Arewa).
"Muna ba da hakuri sosai a kan kuskuren da ya faru a lokacin da aka gabatar da tawagar Koriya ta Kudu a yayin bikin bude gasar Olympics," a cewar hukumar IOC a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X bangaren harshen Koriya.
Kuskuren ya janyo martanin bayyana rashin jin dadin faruwar lamarin a Koriya ta Kudu, kasar da har yanzu ta ke takaddama da Koriya ta Arewa mai makaman nukiliya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar wasanni ta Koriya ta Kudu ta bayyana “takaici" a kan gabatarwar a yayin bikin bude gasar ta Olympics ta shekarar 2024 a birnin Paris.
Mataimakin ministan wasannin kasar Jang Mi-ran, zakaran da ya lashe lambar yabo ta daukar abu mai nauyi a gasar Olympics ta shekarar 2008, ya nemi ganawa da shugaban hukumar IOC, Thomas Bach, domin tattaunawa kan lamarin a cewar sanarwar.
Hakazalika, ma’aikatar wasannin kasar ta bukaci ma’aikatar harkokin wajen koriya ta kudu ta kalubalanci hukumomin Faransa akan batun.
Hukumar wasannin Olympics ta Koriya ta Kudu na sa ran ganawa da hukumar wasannin Olympics ta Paris da kuma hukumar IOC domin bayyana rashin jin dadinsu, ta kuma nemi a dauki matakan hana sake aukuwar hakan nan gaba.
An dai gabatar da ‘yan wasan Koriya ta Arewa daidai da sunan kasar.
Dangantaka tsakanin Koriyoyin biyu ta yi tsami a cikin shekarun nan, yayin da Koriya ta Arewa ke karfafa dangantakar soji da Rasha tare da sakin dubban balan-balan dauke da tarkacen bola a Koriya ta Kudu.
A matsayin maida martani, sojojin Seoul na sanya wakokin kasar Koriya a kan iyakar kasashen da baza rubuce-rubucen sakonnin nuna adawa da gwamnatin makwabiyarta a yankin koriya ta arewa, kuma a kwanan nan ta koma yin atisayen harbe-harbe a tsibiran da ke kan iyaka da kuma kusa da yankin da ba a ayyukan soji da ya raba mashigin koriyoyin biyu.