Hukumar UNFPA Zata Bada $2.5 Domin Kula da Lafiyar Mata Da Kananan Yara a Nigeriya

UNFPA

Cibiyar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA tace zata taimaka da dala miliyan biyu da rabi domin kula da lafiyar iyaye mata da kananan yara
Cibiyar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA tace zata taimaka da dala miliyan biyu da rabi domin kula da lafiyar iyaye mata da kananan yara.

Shugabannin cibiyar UNFPA ne suka fadi haka yayinda suke sa hannu a yarjejeniyar hada hannu domin yin aiki, tare da ma’aikatar lafiya ta kasa. Bisa ga bayanan su, za a bada kudin ne domin kula da lafiyar iyaye da ‘ya’ya daga shekara ta 2013 zuwa 2017 karkashin shirin kula da lafiya na wannan cibiyar.

Ucibiyar NFPA ta kara da cewa shirin zai taimaka wajen shawo kan mutuwar mata 700,000 da kananan yara kusan miliyan daya da dubu dari biyar a kasar, hadi da kara samar da shirin lafiya mai kyau.

Yayin sa hannu a yarjejeniyar direktan shirin lafiya matakin farko Dr. Ado Muhammad yace a cibiyarsu karkashin gwamnatin tarayya ta dauki kimanin ma’aikatan lafiya kusan 10,000 kamarsu unguwar zoma, masu jiyya, da ma’aikatan lafiya a kauyyuka.

Muhammad yace fiye da kayan aikin lafiya 2,000 suka isa kananan hukumomi 459 a kasa gaba daya, a dalilin taimakon wannan kungiyar. Ya kara da cewa ta wurin wani shiri da ake kira SURE P, wanda aka shirya domin ya kara shirye shiryen lafiya, mata da kananan yara suna samun kulawa mai kyau.

Dr Muhammad ya bayyanawa cewa Nigeriya tana da fiye da wuraren kiwon lafiya dubu 25,000 a kasar gaba daya.