Gough tace talauci da rashin ilimi sune muhimman abubuwan dake kawo rashin cin abinci mai inganci a yawancin kasashen afrika, ta kara da cewa UNICEF na shirye ta tanada bayanai kan irin kayan abincin yara ga mata.
Kuma tayi alkawarin cewa UNICEF a shirye take kowanne lokaci ta yi maganin wannan kalubala. Ta bayyana cewa, hukumar tana bada taimako domin kananan yara da iyayensu mata a kasashe dake tasowa.
Ta kara da cewa kungiyar zata bude wani ofishi a Maiduguri domin taimakon gwamnati kawarda cutar shan inna, bada bayani kan rashin abinci nagari da kuma kiwon lafiya. Tace ofishin dake Bauchi yayi nisa daga Borno, don haka suke bukatar bude wani a Maiduguri.
A nashi jawabin gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya bayyana cewa, gwamnatin zata hada hannu da UNICEF domin yaki da shan inna da kuma samar da abinci mai gina jiki ga mata da kuma kananan yaran. Ya kuma ce jihar ta kirkiro shirin cida dalibai a makarantu domin tabbatar da kowanne dalibi ya sami abinci mai kyau.