Kamfannin Facebook zai fuskanci tara daga hukumar dake sa ido kan sahihancin bayanan da kamfanoni ke bayarwa na tarayar Turai, biyo bayan zargin da akewa Facebook kan bayar da bayanai marasa inganci game WhatsApp shekaru uku da suka gabata.
Biyo bayan wani bincike da hukumar ta gudanar na tsawon watanni shida, yanzu haka ana kyauta tsammanin hukumar zata ci tarar Facebook wanda zai zamanto jan kunne ga sauran kamfanoni dake fuskantar irin wannan matsala.
Shugabannin hukumar da kuma kamfanin Facebook baki daya sun ki magana da manema labarai kan batun.
A lokacin da Facebook ke cinikin sayen kafar WhatsApp a shekara ta 2014, Facebook ya fadawa hukumar cewa ba zai iya hada bayanan mutane ta kafofin sadarwar waje ‘daya ba.
Sai gashi hukumar ta gano cewa ko da a wancan lokacin Facebook zai iya hade mutane ta kamfanonin biyu waje ‘daya.
Jami’an hukumar sun gana a wannan makon kan batun, ana kuma tsammanin zasu iya yanke shawara cikin mako mai zuwa.
Your browser doesn’t support HTML5